Dan wasan Southamton Virgil van Dijk zai koma Liverpool ranar 1 ga Janairu da zarar an bude kasuwar cinikin 'yan wasa a kan fam miliyan 75.
Tun bara ake sa ran dan wasan dan asalin Holland zai koma Liverpool bayan da shi da kansa ya nemi a sayar da shi.
Amma hakan bai yiwu ba saboda an tuhumi Liverpool da zawarcin dan wasan ba tare da sanin kungiyarsa ba.
Kudin da za a biya Southampton ya fi na kowane dan wasan baya da aka taba saya a duniya.
Benjamin Mendy da Manchester City ta biya Monaco fam miliyan 52 a watan Yuli shi ne dan wasan baya mafi tsada kafin cinikin Dijk.
Van Dijk ya ce yana alfaharin komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallo a duniya
A wata sanarwa da ya fitar, Van Dijk ya bayyana farin cikin komawarsa Liverpool.
"Ina matukar farin cikin komawa Liverpool a matsayin dan wasa. Yau rana ce ta alfahari a gare ni da iyalina a yayin da na ke shirin komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya."
"Na zaku da in saka jar rigar Liverpool da ta shahara a karon farko a gaban 'yan kallo, kuma na yi alkawarin sadaukar da kaina wajen taimaka wa wannan kungiyar cimma burinta a shekaru masu zuwa."
Source: BBC Hausa
Title :
Liverpool Tasayi Virgil Van Dijk Daga Southampton
Description : Dan wasan Southamton Virgil van Dijk zai koma Liverpool ranar 1 ga Janairu da zarar an bude kasuwar cinikin 'yan wasa a kan fam miliyan ...
Rating :
5