Jose Mourinho ya bukaci Manchester United ta ware ma sa wasu karin kudade domin cefanen sabbin 'yan wasa.
Mourinho ya ce kudaden da ya kashe sama da fam miliyan 300 tun zuwansa Manchester United a watanni 18 sun yi kadan.
Mourinho ya fadi haka ne bayan Burnley ta rike shi 2-2 a Old Trafford.
Kocin ya ce idan har United za ta sha gaban City, to dole sai ta kara kashe kudi a kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu.
Tazarar maki 15 yanzu Manchester City ta ba Manchester United a teburin Premier.
Mourinho ya ce yana iya datse yawan makin da City ta ba United idan har ya yi zubin sabbin 'yan wasa.
Amma wasu magoya bayan Manchester United na ganin kudaden da Mourinho ya kashe sun isa ace ya gina kungiyar.
Kocin City Pep Guardiola ya fi Mourinho kashe kudi a kasuwar musayar 'yan wasa da ta gabata.
Kuma yanzu nasarorin da Manchester City ke samu ne a bana suka shafe duk wani kokarin da Mourinho ke yi a United.
A kakar da ta gabata Mourinho ya lashe wa Manchester United kofuna biyu, kuma a bana yana matsayi na biyu a teburin premier.
Source: BBC Hausa
Title :
Kudaden Dana Kashe A Manchester Basu Isaba-Mourinho
Description : Jose Mourinho ya bukaci Manchester United ta ware ma sa wasu karin kudade domin cefanen sabbin 'yan wasa. Mourinho ya ce kudaden da ya ...
Rating :
5