Kotun Ma'aikata ta kasa wato National Industrial Court a Kaduna ta yanke hukuncin dakatar da korar malaman makarantun Firamare sama da dubu ashirin da gwamnatin jahar Kaduna ta dauri aniyar yi.
Gwamnatin dai ta ce zata yi hakan bayan da malaman suka fadi jarrabawar 'yan aji hudu na Firamare wacce aka yi musu a watan Oktoba.
Alkalin kotun Justice Lawal Mani ne dai ya bada umarnin dakatar da korar har sai lokacin da kotun ta duba tare da yanke tabbatacce hukunci a bisa wannan kara.
Kotun dai dage sauraren karar har zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun 2018.
Daya daga cikin dubban malaman Firamaren da gwamnatin El- Rufa'i ta sallama daga aiki ta ce gwamnatin Kaduna ta yi "diban karan mahaukaciya ne kawai" wajen tantance malaman da ta sallama.
Malamar wadda ta ce ta shafe tsawon kimanin shekara tana koyarwa inda ta kai har matakin shugabar makaranta ta ce sun yi mamaki da jerin sunayen da aka fitar a matsayin wadanda gwamnati ta tantance.
Ta yi ikirarin cewa sunayen wadanda ba su cancanci su fito ba ma, "sun fito, kamar wadanda suka rasu da wadanda suka yi ritaya da masu gadi. Sunayensu sun fito a matsayin wadanda suka cancanci su ci gaba da koyarwa."
Malamar wadda ba ta yarda a kama sunanta ba ta ce akwai mamaki a ce kamar ita, da ke da takardar shaidar malanta ta Grade II da NCE da kuma shaidar karatun digiri amma a ce ba ta cancanci koyarwa ba.
Harkar ilimi a Najeriya al'amari ne da aka dade ana kokawa kan tabarbarewarsa, musamman ma a arewacin kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Kotu Ta Dakatar Da El-Rufai Daga Koran Malaman Firamare
Description : Kotun Ma'aikata ta kasa wato National Industrial Court a Kaduna ta yanke hukuncin dakatar da korar malaman makarantun Firamare sama da d...
Rating :
5