Kotun kolin Amurka ta yanke hukunci kan dokar da Shugaba Donald Trump ya nemi a aiwatar nta haramta wa baki daga wasu kasashen musulmai shida zuwa kasar kwata-kwata, duk da ka cewa har yanzu akwai shari'un da ba a yanke hukunci a kansu ba a wasu kananan kotuna.
Matakin dai zai karfafa manufar Mista Trump ce ta hana mutane daga kasashen Iran da Libya da Syria da Yemen da Somalia da kuma Chadi shiga Amurkan.
Hukuncin ya shafi umarni na uku da shugaba Trump ya bayar game da lamarin tun lokacin da ya dare karagar mulki.
Bakwai daga cikin alkalai tara na kotun kolin kasar sun dage takunkumin da kananan kotuna suka sanya kan aiwatar da dokar.
Masu shari'a da ke da sassaucin ra'yi irin su Ruth Bader Ginsburg da kuma Sonia Sotomayor sun nemi hana aiwatar da dokar, amma ba su yi nasara ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Kotu Ta Amince Da Hana Wasu Musulmai Shiga Amurka
Description : Kotun kolin Amurka ta yanke hukunci kan dokar da Shugaba Donald Trump ya nemi a aiwatar nta haramta wa baki daga wasu kasashen musulmai shid...
Rating :
5