Ya fi Cristiano Ronaldo da Neymar da kuma West Brom da Crystal Palace - yawan kwallaye a shekarar 2017.
Iya zura kwallo a raga na dan wasan gaban Tottenham din ya ci gaba ranar Asabar inda ya ci kwallo biyu a wasan da Spurs ta lallasa Stoke da 5-1 a filin wasa na Wembley.
Kane ya ci kwallo 33 cikin wasannin gasar Firimiya 32, wadanda suke cikin kwallaye 50 da ya ci cikin wasanni 48 a dukkan gasa da ya buga wa kulob dinsa da kasarsa
Dan shekara 24 din ya yi kusa da tarihin da mutumin da ake ganin Kane zai gada ya kafa- tsohon dan wasan gaban Blackburn da Newcastle da kuma Ingila, Alan Shearer.
Wadanda suka fi cin kwallaye a gasar Firimiya a shekara cikin tarihi
Dan wasaKulobKwallayeShekaraAlan ShearerBlackburn361995Robin van PersieArsenal352011Thierry HenryArsenal342004Harry KaneTottenham332017Alan ShearerBlackburn301994Les FerdinandNewcastle301995Ruud van NistlerooyManchester United302003
Kwallayen Kane 33 suna daidai da ko kuma sun fi na kungiyoyin kwallon kafar gasar Firimiya a wannan shekarar - na Swansea da Burnley (jumulla sun da 33), Crystal Palace (tana da 31) kuma West Brom (tana da 30).
Kwallaye biyun da Kane ya ci Stoke sun sa jumullar kwallayen da ya ci a gasar Firimiya sun kai 90, matakin da ya cimma cikin wasanni 131.
Shearer kadai ne kawai fi saurin kai wannan matakin a tarihin gasar Frimiya , inda ya kai matakin cikin wasanni 113 kafin ya kai ga kafa tarihin cin kwallaye 260 a wasanni 441 .
Shearer ya cigaba da taka leda har ya kai shekara 35. Idan Kane ya cigaba da murza leda har ya kai wadannan shekaraun, zai samu damar shekara 11 inda zai nemi cin kwallaye 170 da yake bukata domin kamo iya kwallayen Shearer, abin da zai kai ga in yana cin kwallaye 15 a ko wace kaka har zuwa karshen kakar 2028-29 .
Kane da Shearer - tarihin cin kwallo a kakarsu takwas ta farkoKaneShearerkakaKulobWasanniKwallayeKakaKulobWasanniKwallaye2010-11Leyton Orient (loan)1851987-88Southampton532011-12Millwall (loan)2271988-89Southampton1002012-13Leicester, Norwich (both loan), Tottenham1921989-90Southampton2632013-14Tottenham1031990-91Southampton3642014-15Tottenham34211991-92Southampton41132015-16Tottenham38251992-93Blackburn21162016-17Tottenham30291993-94Blackburn40312017-18 (kawo yanzu)Tottenham1512
Source: BBC Hausa
Title :
Kane Yakusa Kai Alan Shearer Kwallaye
Description : Ya fi Cristiano Ronaldo da Neymar da kuma West Brom da Crystal Palace - yawan kwallaye a shekarar 2017. Iya zura kwallo a raga na dan wasan...
Rating :
5