Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya taya shugaban kasar Muhamadu Buhari jaje game da hatsarin da dansa Yusuf ya yi a kan wani babur na tsere.
Fadar shugaban kasar ta ce Yusuf "ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki" bayan hatsarin da ya yi a unguwar Gwarimpa da ke kwaryar birnin Abuja.
Sai dai ta musanta wani rahoto da ke cewa an kai asibitin kasashen waje domin kula da lafiyarsa.
A wata sanarwa da Goodluck Jonathan ya wallafa a shafinsa na Twitter ya yi addu'ar samun sauki ga Yusuf Buhari, yana mai cewa "Ina kasar Liberia inda nake sa ido kan zaben kasar sai kawai na ji wannan mummunan labari.
"Ni da iyalina muna yin addu'ar saurin samun sauki ga Yusuf Buhari. Ina matukar shaukin ganin wannan matashi wanda ke kan ganiyarsa ya rayu sannan ya cika alkawuran da Allah ya dora masa a matsayinsa na dan adam.", in ji tsohon shugaban.
Shi ma tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar da shugaban majalisar dattawan Najeriya sun jajanta wa Shugaba Buhari kan hatsarin da dansa ya yi.
Source: BBC Hausa
Title :
Jonathan Ya Jajanta Wa Buhari
Description : Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya taya shugaban kasar Muhamadu Buhari jaje game da hatsarin da dansa Yusuf ya yi a kan wani babu...
Rating :
5