Rundunar 'yan sandan kasa da kasa ta Interpol ta kwace jabun magunguna miliyan 25, da darajarsu ta kai kudi dala miliyan 51 a wani farmaki da jami'anta suka kai cikin mako guda a fadin duniya.
A watan Satumban bana ne rundunan 'yan sandan ta kaddamar da samamen a kasashe 123, kuma 26 daga ciki daga kasashen Afirka ne.
Wata guda kafin wannan samamen, 'yan sanda sun cafke kwaya miliyan 41 da suka kai darajar kudi dala miliyan 22 a yammacin Afrika kadai.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce kusan kashi 30 cikin 100 na magungunan da ake samarwa a wasu yankunan Afirka na jabu ne. kuma daya cikin 10 na kamfanonin da ke yin magungunan a kasashen masu tasowa ba su da wani inganci.
Hukumomin da ke sa ido kan harkar samar da magunguna a Najeriya, sun ce suna aiki kafada da kafada da 'yan sandan na Interpol don kawo karshen samar da magungunan na jabu, duk da cewa har yanzu ana sayar da jabun magungunan a ciki da wajen kasar.
'Yan sandan na Interpol sun kaddamar da samamen a wata kasuwar sayar da jabun magunguna a bainar jama'a a Lagos.
Wakiliyar BBC Didi Akinyelure da ta bi tawagar jami'an da ke sa ido kan samar da magunguna a samamen, ta ce an cafke masu sayar da magungunan da dama tare da kwace magungunan da suke sayarwa.
"Yan sandan sun tunkari kasuwar ne rike da manyan bindigogi" a cewar wakiliyar BBC.
Sannan ta ce 'Yan sandan sun yi harbi sama domin razana su a lokacin da suka isa kasuwar Idimota a Lagos, bayan 'yan kasuwar maganin sun yi kokarin tserewa.
Ire-iren magungunan da aka kama
Yawanci magungunan karfin maza ne aka kama da kuma masu kara sanya sha'awa, kamar Viagra.
Daya daga cikin Jami'in NAFDAC da wakiliyar BBC ta zanta da shi, ya ce kasuwar maganin karfin maza tana ci sosai. Sannan akwai magungunan da ke sa maye cikin wadanda aka kama irinsu Kodin da Tiramol da wasu nau'in magungunan rage radadi da kuma wasu na ciwon ido.
Wakiliyar BBC ta ce duk da akwai gargadin bukatar a ajiye magungunan a wuri mai sanyi amma yawanci ana adanawa da sayar da magungunan a cikin rana a yanayin da ya kai maki 30 na ma'aunin selshiyos.
Akwai dai magunguna da dama da aka gano sun lalace a kasuwar.
Kusan shekaru sama da 50 ke nan, da wannan kasuwar bayan fage ta magunguna ke ci a Lagos. Akalla akwai sama da kananan shaguna 80 a yankin, yawancinsu ba su da rijistar samar da magunguna a hukumance.
Ko da yake duk da cewa ba duka ne hukuma ta san da zamansu ba, amma akwai tsiraru da ke sayar da magunguna masu inganci, dalilin da ya sanya hukumomi suka gagara rufe shagunan.
Kuma yawancin magungunan jabu da ake sayarwa a kasuwar ana shigo da su ne daga kasashen yankin Asia ta barauniyar hanya.
Yawancin kamfanonin magunguna a Najeriya ba su sayarwa asibitoci kai-tsaye, sai dai su saya a kasuwar, ko kuma su karba a hannun diloli, wanda hakan ya ba masu sayar da maganin jabu shigar da hajarsu.
Dakta Awosika ya ce ya shafe shekaru 30 yana aikin likitanci, kuma a can baya suna sayen magunguna kai tsaye daga kamfanin da suke hadawa, amma daga baya ne lamarin ya tabarbare, dole ya koma saye a hannun 'yan kasuwa.
Ya kara da cewa matsalar ita ce takamaimai ba su san daga inda 'yan kasuwar ke samun maganin ba.
"Kawai ana kawo su kai tsaye a asibiti mu kuma mu yi amfani da su" a cewar Dakta Awosika wanda likitan fida ne.
Sannan ya ce ya taba shiga wani tashin hankali, a lokacin da ya ke aikin tiyata, ana cikin aiki sai marar lafiyan ya farka, wanda hakan ke nuna allurar da aka masa nan take ta sake shi kafin ainihin lokacin da ya dace, al'amarin ya firgita shi, saboda bai taba ganin haka ba.
Akwai kuma Vivian Nwakah, shugabar kamfanin Medsaf a intanet inda ta bayyana halin da ta taba samun kanta sanadiyyar magungunan jabu.
Vivian ta ce ta dauki tsawon lokaci tana shan wani magani da aka samar a Najeriya, amma sam ba ya aiki. Abin da kara ya ba ta tsoro da firgita, shi ne lokacin da wata kawarta ta sha maganin zazzabin cizon sauro na jabu, kuma ta rasu.
Wannan ne ya sa Vivian ta sha alwashin cewa ba za ta taba yadda wani ya shiga halin da ta shiga ba, wanda ya zaburar da ita domin yakar sayar da magungunan jabu da marasa inganci.
Aikin da shafin Medsaf na Vivian ke yi, ya shafi tabbatar da hada asibitoci da kamfanonin magunguna masu inganci. Kawo yanzu kusan jami'an lafiya 300 ne suka shiga fafutukar, sai dai adadin ya yi kadan ana bukatar karin mutane don magance matsalar.
Hukumomin Najeriya dai sun ce suna aiki kafada da kafada da gwamnatin India da China don karya lagon masu shigo da magunguna a cikin kasar daga ketare, suna kuma kokarin ganin sun rufe wannan kasuwar jabun magungunan a karshen shekara mai zuwa inda kafin zuwan lokacin, za a ci gaba da kai samame a irin wadannan kasuwannin a duk fadin kasar.
Source: BBC Hausa