Shugaba Trump na Amurka, ya yi barazanar yanke taimakon kudi ga kasashen da suka juya wa Amurka baya a kuri'ar da za a kada kan batun birnin Kudus a wajen taron koli na Majalisar Dinkin Duniya.
Daftarin da aka mika wa Majalisar Dinkin Duniya wanda wasu kasashe da ke adawa da matakin Mr Trump, suka gabatarwa majalisar, bai ambaci sunan Amurka ko kuma shugaba Trump ba, sai dai ya ce duk wani yunkuri a kan Kudus a soke shi.
A farkon watan da muke ciki ne Mr Trump, ya dauki matakin mayar da Kudus babban birnin Isra'ila, lamarin da ya samu suka daga kasashen duniya.
Mr Trump, ya yi wannan barazana ce gabanin taron koli na Majalisar Dinkin Duniya inda za a kada kuri'a kan batun birnin Kudus.
Taron zai duba shawarar da za ta ki amincewa da matakin da Mista Trump ya dauka, na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.
Mr Trump, dai ya bayyana matakin da ya dauka na mayar da birnin Kudus babban birnin Isra'ila, a matsayin wani abu da aka dade ba a yi ba a kokarin karfafa zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Shugaban na Amurka, ya ce: "Naji dadin sakon da Nikki ta isar a Majalisar Dinkin Duniya ga dukkan kasashen da suke karbar taimakon miliyoyin kudin Amurka, amma kuma suka kada kuri'ar da za ta yi wa ra'ayina yankan baya.
"Suna karbar kudinmu sannan kuma suna kin zabar mu, muna kallon irin wadannan kasashe. Su je kada su zabe mu, mu gaba ta kai mu domin za mu samu damar adana makudan kudade, don haka can ga su gada".
Tun da farko dai jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley, ta gargadi mambobin kungiyar a kan cewa, Shugaba Trump ya shaida mata cewa ta bayar da rahoto a kan duk wata kasa da ta juyawa Amurka baya a kan wannan mataki a taron majalisar da za a yi, inda za a kada kuri'a kan batun birnin Kudus a ranar Alhamis.
Isra'ila dai ta dauki birnin Kudus a matsayin babban birininta, yayin da Falasdinawa suka ayyana gabashin Kudus a matsayin wurin da zai kasance babban birninsu idan sun kafa tasu kasar.
Kasashen duniya dai ba su taba daukar cewa Isra'ila ce ke iko da Birnin Kudus ba, kuma dukkan kasashen duniyar na da ofishin jakadancinsu ne a Tel Aviv.
To sai dai kuma tuni Shugaba Trump, ya sanar da ma'aikatar harkokin wajen kasarsa cewa ta fara shirye-shiryen mayar da ofishin jakadancinsu zuwa Kudus daga Tel Aviv.
A ranar Alhamis ne, kasashe mambobin majalisar dinkin duniya 193, za su yi wani taron gaggawa a kan bukatar hakan wanda kasashen Larabawa da kuma kasashen musulmai wadanda suka soki matakin Mr Trump suka gabatar.
Falasdinawa ne suka kira taron bayan da Amurka ta hau kujerar naki a kan wani daftarin kudirin Majalisar Dinkin Duniya da ke kira da a sauya shawarar da Shugaba Trump ya yanke, wadda ta bayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.
Ministan harkokin wajen Falasdinu Riyad al-Maliki, da takwaransa na Turkiyya Mevlut Cavusoglu, sun zargi Amurka da yin barazana.
Mr Cavusoglu ya ce: "Mun ga cewa Amurka wadda aka juyawa baya aka barta ita kadai, yanzu ta koma yin barazana. Babu wata kasa da wannan barazana za ta sanyayawa gwiwa".
Amincewar da Amurka ta yi wa Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, ya sa ta kasance kasa ta farko da ta yi haka tun bayan kafuwar Isra'ilar a shekarar 1948.
Wannan mataki da Mr Trump ya dauka, ya sa dubun-dubatar mutane a kasashe daban-daban na duniya gudanar da zanga-zangar adawa a kan matakin.
Birnin Kudus, yana da muhimmanci ga 'yan Isra'ila da Falasdinawa.
Birnin, na kunshe da wurare masu tsarki na manyan addinai guda uku - Yahudanci da Islama da addinin Kirista.
Isra'ila ta mamaye bangaren Gabas wadda a da ke karkashin mamayar Jordan a shekarar 1967, aka kuma kwace a 1980, amma duniya ta yarda da hakan.
Falasdinawa 330,000 ne suke zaune a Gabashin Kudus, tare da kusan Yahudawa 200,000 a gomman matsugunai a wajen.
Source: BBC Hausa
Title :
Ina Sane Da Kasashe Dasuka Juya Mana Baya Kan Kudu-Trump
Description : Shugaba Trump na Amurka, ya yi barazanar yanke taimakon kudi ga kasashen da suka juya wa Amurka baya a kuri'ar da za a kada kan batun bi...
Rating :
5