Harry Kane ya zura kwallo uku rigis, ya kuma kawar da tarihin bajintar cin kwallo mafi yawa a Premier a cikin shekara bayan da Tottenham ta caskara Southampton a Wembley 5-2.
Dan wasan na gaba na Tottenham da Ingila ya ci bal dinsa ta 37 a Premier a wannan shekara ta 2017 a minti 22 da wasa, ya wuce bajintar da Alan Shearer ya yi, lokacin yana Blackburn a 1995.
Daga nan ne kuma Kane din ya kara biyu kafin tafiya hutun rabin lokaci a minti na 39 sannan kuma bayan an dawo ya ci ta uku a minti na 67, abin da ya kawo jumullar yawan kwallon da ya ci wa kungiyarsa da kasarsa a shekarar nan zuwa 56, inda ya zarta dan wasan gaba na Barcelona da Argentina Lionel Messi da kwallo biyu.
Kafin kane ya ci bal ta uku Dele Alli shi ne ya ci wadda ta sa wasan ya zama 3-0 a minti na 49.
Minti biyu bayan wannan ne kuma sai ya ba wa Son Heung-min wanda shi ma ya kwarara tasa a raga a minti na 51.
Southampton, wadda ta kasance ba tare da gwanin ci mata kwallo ba Charlie Austin, ta farfado lokacin da Sofiane Boufal ya ci mata daya a minti na 64.
Sannan kuma Dusan Tadic ya kara ci mata ta biyu ana minti 82 da wasa bayan da dan wasan ya sheko bal din da ta wuce golan Tottenham Hugo Lloris.
Daga nan kuma bakin ba su kara daga raga ba, abin da ya sa yanzu suka kai wata daya ba tare da sun ci wasansu ba a gasar ta Premier.
Yanzu Tottenham ta tsaya a ta biyar a tebur bayan da Liverpool wadda ta jaddada zamanta a matsayi na hudu bayan da ta lallasa bakinta 'yan Swansea 5-0 a wasan na Talata.
Sakamakon sauran wasannin Premier na Talata:
Bournemout 3-3 West Ham
Chelsea 2-0 Brighton
Huddersfield 1-1 Stoke
Man Utd 2-2 Burnley
Watford2-1 Leicester
West Brom 0-0 Everton
A ranar Laraba 27 ga watan nan na Disamba Newcastle United za ta karbi bakuncin jagora a gasar ta Premier Manchester City, inda za su fara karawar da misalin karfe 8:45 agogon Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Harry Kane Yawuce Messi Da Alan Shearer Cin Kwallaye
Description : Harry Kane ya zura kwallo uku rigis, ya kuma kawar da tarihin bajintar cin kwallo mafi yawa a Premier a cikin shekara bayan da Tottenham ta ...
Rating :
5