Marek Hamsik ya buge tarihin da Diego Maradona tsohon dan wasan Argentina ya kafa na wanda yafi cin kwallaye a Napoli.
Napoli ta yi nasarar doke Sampdoria 3-2 a ranar Asabar a wasan mako na 18 a gasar cin kofin Serie A karawar mako na 18, kuma hakan ya sa ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi.
Kyaftin din Napoli, Marek Hamsik shi ne ya ci kwallo na uku tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, kuma na 116 da ya ci wa kungiyar a wasa 465 da ya buga mata.
Tun a makon jiya ya yi kan-kan-kan da Maradona a yawan cin kwallaye a fafatawar da Napoli ta doke Torino 3-1, bayan ya buga wasa 13 bai ci kwallo ba a kungiyar.
Napoli ita ce ta daya a kan teburin Serie da maki 45, bayan wasa 18 da ta yi.
Source: BBC Hausa
Title :
Hamsik Ya Buge Tarihin Maradona
Description : Marek Hamsik ya buge tarihin da Diego Maradona tsohon dan wasan Argentina ya kafa na wanda yafi cin kwallaye a Napoli. Napoli ta yi nasarar...
Rating :
5