Gwamnonin jihohin Najeriya sun goyi bayan a kashe kudi dala biliyan daya domin yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari shugaban gwamnonin jihohin kasar 36 ne ya sanar da matakin a taron majalisar zartarwa da aka gudanar, wanda Farfesa Yemi Osibanjo ya jagoranta a fadar shugaban kasa a Abuja.
Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya shaidawa manema labarai cewa gwamnonin sun amince gwamnatin Tarayya ta kashe kudi dala biliyan daya domin yakar Boko Haram.
Za a dai kashe kudaden ne daga asusun rarar kudin mai na kasar.
Gwamnonin sun ce sun amince a kashe kudaden ne saboda ci gaban da aka samu a yaki da Boko Haram.
Boko Haram dai na ci gaba da zama barazana a arewa maso gabashin kasar, inda mayakan kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake tare da kashe fararen hula.
Gwamnonin kuma sun tattauna matsalar karancin fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya, inda karamin ministan albarkatun mai ya yi alkawalin cewa za a kawo karshen matsalar nan da sa'o'i 48.
Har yanzu ana fama da dogayen layi a gidajen mai a manyan biranen Najeriya, kasar da ta fi arzikin mai a nahiyar Afirka.
Source: BBC Hausa
Title :
Gwamnoni Sun Amince Akashe Dala Biliyan 1 Don Yakan Da Boko Haram
Description : Gwamnonin jihohin Najeriya sun goyi bayan a kashe kudi dala biliyan daya domin yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar. Gwa...
Rating :
5