Wata gobara da ta tashi a wani wajen motsa jiki a Koriya ta Kudu ta kashe mutum 29 kuma ta jikkata wasu mutanen da dama.
Gobarar, wadda ta faro a ginin karkashin kasa na bene mai hawa takwas, ta yi barna sosai a birnin Jecheon da ke kudancin kasar.
Hotunan bidiyon gobarar sun nuna yadda bakin hayaki ya turnuke yayin da wutar ta kama ginin.
Yawancin wadanda abin ya rutsa da su sun makale ne a wani karamin daki da ke da hawa na biyu na ginin.
Jami'ai sun ce yawan wadanda suka mutu zai iya karuwa yayin da 'yan kwana-kwana suke ci gaba da ceto mutane.
"Wutar ta haifar da hayaki mai guba cikin gaggawa, lamarin da ya sa mutane da dama ba su iya barin wurin ba," in ji wani mai magana da yawun hukumar 'yan kwana-kwanan kasar.
An ceci mutum 20 ta saman benen bayan sun tsere daga wutar.
Da yawa daga cikin wadanda suka tsira an kai su asibiti domin a yi musu magani na hayakin da suka shaka, in ji jami'ai.
Jami'an dai sun kara da cewa ma'aikatan kashe gobara da dama sun hallara a wajen ranar Alhamis, a cikin birnin da ke da nisan kilomita 168 a kudancin birnin Seoul.
Hayaki mai yawa yana cigaba da kawo cikas ga aikin ceto, in ji hukumomi.
Ginin yana dauke da wata cibiyar motsa jiki da wuraren sayar da abinci da kuma wani daki da ke ba da dumi.
Source: BBC Hausa