Mutane 12 ne suka mutu a lokacin da wata gobara ta tashi a gundumar Bronx da ke birnin New York din Amurka.
Magajin birnin Bill De Blasio ya ce an samu shawo kan gobarar, ya kuma ce wasu mutane 4 na kwance a asibiti saboda kunewar da suka yi.
Mista De Blasio ya ce wannan ce gobara mafi muni da birnin ya fuskanta cikin shekara 25.
Wani mutumin ya ga abin da ya faru, ya ce wutar ta na ci balbal ya yin da mutanen da ke cikin gidajen da ta shafa su ke gudun ceton rai.
Mutane sun yi ta fitowa daga gidajensu, wasu babu ko sutura wasu kuma sanye da kayan bacci.
A bangare guda kuma jami'an kashe gobara sun dukufa dan shawo kan ta, ya yin da aka garzaya da wadanda suka kone asibiti.
Hukumomi sun ce ya yi wuri a gano musabbabin tashin gobarar, amma su na gudanar da bincike.
Source: BBC Hausa
Title :
Gobara Ta Hallaka Mutane 12 A Amirka
Description : Mutane 12 ne suka mutu a lokacin da wata gobara ta tashi a gundumar Bronx da ke birnin New York din Amurka. Magajin birnin Bill De Blasio y...
Rating :
5