Akalla fursunoni 36 ne suka tsere daga gidan yarin garin Ikot Ekpene da ke jihar Akwa-Ibom a kudu maso kudancin Najeriya bayan sun fasa gidan.
Wata sanarwa daga jami'in hulda da jama'a na rundunar gandirobobin jihar Ogbajie J. Ogbajie ya fitar ta ce fursunonin da suka fasa gidan yarin sun kwace gatari daga masu dafa abinci daga cikinsu suka yi amfani da shi wajen kai musu hari har suka ji musu ciwo a ka.
Sanarwar ta ce daga nan sai suka afka wa kofar baya ta gidan yarin da gatarin suna masu gumurzu da jami'an tsaron gidan da suka bi su.
Kazalika sanarwar ta ce bayan rikicin ya lafa dai hudu daga cikin fursunonin sun mutu daga raunukan da suka ji sakamakon harbin bindiga kuma an kamo bakwai daga cikinsu, yayin da 36 suka tsere.
Shugaban rundunar jami'an gidan yari na jihar, Alex Oditah, ya bayar da umarnin bincika yadda aka fasa gidan yarin.
Ana samun irin yanayin da fursuna ke fasa gidan yari a Najeriya inda ake samun cinkoso da yawa, yayin da mafi yawa daga cikin mutane da ke gidan yarin suna jiran shari'a ne.
Source: BBC Hausa
Title :
Fursinoni 36 Sun Gudu Daga Gidan Yari
Description : Akalla fursunoni 36 ne suka tsere daga gidan yarin garin Ikot Ekpene da ke jihar Akwa-Ibom a kudu maso kudancin Najeriya bayan sun fasa gida...
Rating :
5