Dan wasan tsakiyar Manchester City Phil Foden zai yi jinyar kusan wata hudu sakamakon raunin da ya yi.
Foden mai shekara 17, ya taka leda a minti na 89 na fafatwar da kungiyarsa ta yi nasara a kan Leicester a gumurzun da suka yi ranar Talata, kuma taka ledarshi na hudu a kungiyar a bana.
Foden ya fafata a wasan da Ingila ta lashe gasar kofin duniya na 'yan kasa da shekara 17 a watan Oktoba.
Kocin kungiyar Pep Guardiola ya ce abin takaici ne rashin dan wasan na tsawon wannan lokacin
A ranar Asabar ne City za ta kara da Bournemouth a filin wasa na Etihad, ranar 27 ga watan Disamba kuma za ta karbi bakuncin Newcastle.
City ita ce ta farko a teburin Firimiya da maki 51.
Source: BBC Hausa
Title :
Foden Yatafi Hutun Jinya
Description : Dan wasan tsakiyar Manchester City Phil Foden zai yi jinyar kusan wata hudu sakamakon raunin da ya yi. Foden mai shekara 17, ya taka leda a...
Rating :
5