Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi gargadi ga hukumar kwallon Spain kan yadda gwamnatin kasar ke katsalandan ga sha'anin zaben shugabancin hukumar.
Rahotanni sun ce gwamnatin Spain ta tuntubi hukumar kwallon kafar kasar kan batun wanda ta ke son ya maye gurbin tsohon shugaban hukumar Angel Maria Villar wanda ya yi murabus a watan Yuli saboda zargin rashawa.
A tsarin FIFA, ana na iya dakatar da wakilcin kasar da gwamnati ta yi katsalandan a sha'anin zaben shugabannin hukumar kwallon kafa.
FIFA ta aike da wasikar gargadi ga hukumar kwallon Spain, tana mai yin kashedi ga duk wani mataki na tsoma bakin gwamnati.
Idan har hakan ta tabbata, FIFA na iya korar Spain daga gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a 2018.
FIFA ta fadi a cikin wata sanarwa cewa za ta tura tawagar jami'anta da na hukumar kwallon kafar Turai UEFA zuwa Madrid domin gudanar da bincike tare da sa ido ga sha'anin hukumar kwallon kafar Spain.
Shugaban hukumar kwallon Spain na rikon kwarya Juan Luis Larrea ya tabbatar da cewa sun karbi takardar gargadin daga FIFA, kuma ya ce sun gabatar da sakon ga ministan wasannin kasar.
Kaftin din Spain Sergio Ramos ya ce ba zai taba yadda ace Spain ta rasa abin da suka yi fafutika ba.
Spain dai ta taba lashe kofin duniya da aka gudanar a Afirka ta kudu a 2010, kuma ko yanzu kasar na cikin kasashen da ake ganin za su iya lashe kofin gasar da za a gudanar a Rasha a badi.
A 2015 FIFA ta taba haramtawa Indonesia buga wasannin neman zuwa gasar cin kofin duniya saboda tsoma bakin gwamnati a harakokin hukumar kwallon kafar kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Fifa Ta Gargadi Spain Akan Zuwa Rasha
Description : Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi gargadi ga hukumar kwallon Spain kan yadda gwamnatin kasar ke katsalandan ga sha'anin zaben sh...
Rating :
5