Kila a yi wa dan wasan baya na Manchester United Eric Bailly aiki a kafarsa sakamakon tsananin raunin da ya ji in ji kociyansu Jose Mourinho.
Dan wasan mai shekara 23 wanda Mourinho ya ce ya ji rauni a idon sawu lokacin da ya je buga wa kasarsa Ivory Coast wasa, bai taka wa United leda ba tun lokacin da Chelsea ta ci su a gidanta a ranar biyar ga watan Nuwamba.
Ba dai a jin jinyar za ta kai shi ga rasa sauran wasannin da kungiyar za ta yi a kakar nan.
Mourinho ya ce a yanzu suna jarraba wasu hanyoyi na maganin raunin kamar yadda aka saba amma idan ya ci tura to dole sai an yi masa aiki.
A rashin dan wasan yanzu kociyan ya ce yana amfani da Chris Smalling da Phil Jones kamar yadda ya sa su a wasan jiya Laraba da suka ci Bournemouth 1-0, kuma ya ce yana jin dadin hadin.
Bailly shi ne dan wasan farko da United ta sayo daga Villareal a bazarar 2016 a kan fam miliyan 30, bayan da Mourinho ya zama kociyanta.
Source: BBC Hausa
Title :
Eric Bailly Yaji Rauni Sosai-Mourinho
Description : Kila a yi wa dan wasan baya na Manchester United Eric Bailly aiki a kafarsa sakamakon tsananin raunin da ya ji in ji kociyansu Jose Mourinho...
Rating :
5