Daya daga cikin dubban malaman Firamaren da gwamnatin El- Rufa'i ta sallama daga aiki ta ce gwamnatin Kaduna ta yi "diban karan mahaukaciya ne kawai" wajen tantance malaman da ta sallama.
Malamar wadda ta ce ta shafe tsawon kimanin shekara tana koyarwa inda ta kai har matakin shugabar makaranta ta ce sun yi mamaki da jerin sunayen da aka fitar a matsayin wadanda gwamnati ta tantance.
Ta yi ikirarin cewa sunayen wadanda ba su cancanci su fito ba ma, "sun fito, kamar wadanda suka rasu da wadanda suka yi ritaya da masu gadi. Sunayensu sun fito a matsayin wadanda suka cancanci su ci gaba da koyarwa."
Malamar wadda ba ta yarda a kama sunanta ba ta ce akwai mamaki a ce kamar ita, da ke da takardar shaidar malanta ta Grade II da NCE da kuma shaidar karatun digiri amma a ce ba ta cancanci koyarwa ba.
Ta yi fatan gwamnatin Kaduna za ta biya su hakkokinsu don ta je ta bude makarantarta mai zaman kanta, inda har ma wasu za ta iya dauka aiki.
"A gaskiya wannan aiki ya fita a raina kwata-kwata. Idan za su biya su ba ni kudaden da suka cancanta su ba ni da basukan watanni da muke bin su, insha Allahu zan je na bude wata makaranta mai zaman kanta."
Sabanin ikirarin gwamnatin Kaduna, malamar ta ce ta cancanci aikin koyarwa bisa la'akari da takardun shaidar malanta da take da su.
Ita dai gwamnatin jihar Kaduna ta ba da sanarwar sallamar malaman Firamaren ne su kimanin 22,000 saboda "gaza cin jarrabawar dalibansu 'yan aji hudu" da ta yi musu.
Al'amarin dai ya janyo takaddama a cewar wakilin BBC Ishaq Khalid, inda tuni kungiyoyin kwadago a Kaduna suka ce ba su yarda ba, suna zargin maye guraben malaman da magoya bayan gwamna.
Kungiyoyin kwadagon dai sun shigar da wannan batu gaban kotu, inda jagoran 'yan kwadago a Kaduna, kwamared Adamu Ango ya ce ba a bi ka'ida wajen shirya jarrabawar ba.
Tuni dai gwamnatin jihar ta fara aikin daukar sabbin malamai guda 25,000 don maye guraben wadanda ta sallama.
Babban jami'i na biyu a hukumar ilmin baidaya ta jihar Kaduna, Malam Shehu Sani Usman ya ce malaman ba su da amfani a cikin aji.
Ya ce sun ba su har zuwa watan Fabrairun 2018 don su fice daga makarantun da suke koyarwa.
Source: BBC Hausa