Yusuf Buhari, dan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi mummunan hatsarin babur din tsere a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa da ke birnin ranar Talata da daddare.
A cewar Garba Shehu, "Ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki".
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Buhari da mai dakinsa Aisha suna godiya ga 'yan Najeriya bisa addu'ar da suke yi wa dan nasu.
'Ya'yan masu hannu da shuni kan yi wasan tseren babura akai-akai a wani yanki na kwaryar birnin Abuja, lamarin da ake gani na cike da hatsari.
A shekarun baya, hukumar birnin tarayyar ta haramta yin irin wannan tsere bayan wasu rahotanni da aka samu na tukin ganganci da masu tseren ke yi.
Source: BBC Hausa
Title :
Dan Shugaba Buhari Ya Karye Sanadiyyar Hadarin Babur
Description : Yusuf Buhari, dan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi mummunan hatsarin babur din tsere a Abuja, babban birnin tarayyar kasar. Wata sa...
Rating :
5