Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce akalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a kasar.
Cutar dai ta bulla ne a wani kauye mai suna unguwar Mallam da ke yankin Mirriah a jahar Damagaram.
Wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou wacce ta ziyarci garin ta ce ta tarar iyalai na zaman makokin wadanda suka mutu a gidaje da dama.
Wasu mazauna garin sun ce akasarin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mata ne da kananan yara.
A halin yanzu jami'an kiwon lafiya na ci gaba da samar da allurar rigakafi a cibiyoyi da aka kafa don kula da wadanda suka kamu da cutar.
Source: BBC Hausa
Title :
Cutar Sankarau Kar Mutane 20 A Nijar
Description : Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce akalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a kasar. Cutar dai ta bulla ne a wan...
Rating :
5