Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya ce dan wasansu na gaba Cristiano Ronaldo na bukatar a mutunta shi sosai duk da rashin cin kwallo da yake yi a gasar La Liga a bana.
Kociyan ya ce ya kamata su ba wa Cristiano karin goyon baya da kuma girmamawa.
Ronaldo, mai shekara 32, ya ci kwallo 8 daga cikin 14 da Real ta ci a gasar zakarun Turai a wasannin rukuninsu na takwas (Group H), ya taimaka wa zakarun gasar sau 12 suka kai matakin gaba na gasar a matsayin na biyu a rukunin bayan Tottenham.
Ba wani dan wasa da ya ci yawan kwallon da Ronaldon ya zura a raga a gasar ta zakarun Turai, amma kuma a bana kwallo biyu kawai ya ci a La Liga.
Yayin da Real din ta kai mataki na gaba a matsayin ta biyu a rukunin, Borussia Dortmund, wadda take ta uku za ta samu damar zuwa gasar Europa idan ba ta bari mai rike da kofi Real Madrid ta doke ta ba a karawarsu ta Larabar nan a Bernabeu.
Yanzu dai duk maganganun da ake yi a Spaniya na kafin wasa ana yinsu ne a kan kamfar zura kwallon ta Ronaldo a gasar La Liga, inda maki 8 ke tsakanin Real din da Barcelona ta daya a tebur.
Source: BBC Hausa
Title :
Cristiano Ronaldo Na Bukatan A Mutunta Shi-Zidane
Description : Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya ce dan wasansu na gaba Cristiano Ronaldo na bukatar a mutunta shi sosai duk da rashin cin kwallo da y...
Rating :
5