Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana ziyara a jihar Kano da ke arewacin kasar, a karon farko tun bayan da ya zama shugaban kasa sama da shekara biyu da suka wuce.
Yadda Kanawa suka zabi Buhari
Irin kuri'un da suka kada masa a 2015
9,401,288
Yawan al'ummar Kano
2,172,447 Yawan kuri'un da aka kada a zaben 2015
1,903,999 Kuri'un da Buhari ya samu
215,779 Kuri'un da Jonathan ya samu
INEC da Hukumar Kidayar Jama'a ta Najeriya
Ofishin Shugaban Najeriya
Kano dai ita ce cibiyar siyasar shugaban.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce, Shugaba Buhari "zai yi ziyarar kwana biyu a jihar Kano, babbar cibiyar siyasarsa da inda babu wanda ya isa karawa da shi".
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa Shugaba Buhari zai gana da manyan mutane da dama da kuma kaddamar da ayyukan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aiwatar.
Sai dai mazauna jihar da dama na sukar shugaban saboda abin da suka kira rashin kulawa da jihar da kuma gudanar da ayyukan gwamnatin tarayya duk da ikirarin da yake yi na kaunarta.
Amma wasu magoya bayansa na ganin ko da bai kai ziyara jihar ba, babu abin da zai shafi irin kaunar da suke yi masa.
Tun gabanin zuwan shugaban dai aka tsaurara tsaro a jihar, kana aka rika sanarwa a gidajen rediyo cewa iyaye su ja kunnen 'ya'yansu da su guji tayar da hatsaniya a lokacin ziyarar shugaban kasar.
Wasu masu sharhi a kan sha'anin siyasa na cewa masoyan Shugaba Buhari da gwamnatin Kano za su yi matukar farin cikin ziyarar tasa za ta sa masu yi musu shagube su rufe bakunansu.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Zai Ziyarci Kano A karo Na Farko Tun Bayan Ya Hau Mulki
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana ziyara a jihar Kano da ke arewacin kasar, a karon farko tun bayan da ya zama shugaban kasa sama da s...
Rating :
5