Everton da Chelsea sun tashi wasa babu ci a gasar Premier wasan mako na 19 da suka kara a Goodison Park a ranare Asabar.
Everton ta ci gaba da buga wasanni ba tare da an doke ta ba tun lokacin da Sam Allardyce ya maye gurbin Ronald Koeman.
Everton wacce ke mataki na tara a kan teburin Premier ta yi wasa tara ba a yi nasara a kanta ba, kuma biyar daga ciki Allardyce ne ya jagoranta.
Chelsea wacce ke rike da kofin Premier kuma mai mataki na uku a kan teburin bana ta buga karawar ba tare da Alvaro Morata ba, sakamakon katin gargadi biyar da ya karba a bana.
Chelsea za ta buga wasan mako na 20 a ranar Talata da Brighton, ita kuwa Everton za ta ziyarci West Brom ne.
Source: BBC Hausa
Title :
Everton Tahana Chelsea Shanawa A Gasar Premier
Description : Everton da Chelsea sun tashi wasa babu ci a gasar Premier wasan mako na 19 da suka kara a Goodison Park a ranare Asabar. Everton ta ci gaba...
Rating :
5