An soma shirye shiryen gudanar da bikin cikar binin Kaduna na arewacin Nigeria shekara 100 da kafuwa.
A makon da mu ke ciki ne zaa gudanar da wannan biki, inda za a nuna al'a'dun gargajiya da raye raye da kade da kuma hawan daba .
Sai dai wasu a jihar Kaduna sun nuna rashin jin dadinsu kan bikin da za a yi musaman idan aka yi la'akari da ma'aikatan da aka kora da yanayi kuncin rayuwa da mutane suke ciki a jihar.
Sun ce kamata ya yi a yi zaman makoki a jahar, ba biki ba.
A shekara 1917 aka kafa Kaduna kuma Lord Lugard shi ne gwamnan farko na jihar wanda ya dauko shelkwatar arewa daga Zungeru ya kawota Kaduna.
Bisa la'akari da wannan ne gwamnatin jihar Kaduna ta ce ya kamata ta gudanar da bukukuwa domin murnar cikar jihar shekara 100.
Source: BBC Hausa
Title :
Bikin Cikar Kaduna Shekara 100 Da Kafuwa
Description : An soma shirye shiryen gudanar da bikin cikar binin Kaduna na arewacin Nigeria shekara 100 da kafuwa. A makon da mu ke ciki ne zaa gudanar ...
Rating :
5