Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 3-0 a wasan mako na 17 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu da suka kara a ranar Asabar.
Barcelona ta ci kwallo ta hannun Luis Suarez da Lionel Messi da kuma ta uku da Aleix Vidal ya ci daf da za a tashi daga karawar.
Lionel Messi shi ne yafi cin kwallo a tarihin karawar El Clasico, bayan da ya ci kwallo na 25, guda 15 a Bernabeu kuma 17 a gasar La Liga ta bana.
Real ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Dani Carvajal jan kati sakamakon taba kwallo da hannu a cikin da'ira ta 18 din Madrid
Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga da maki 45, ita kuwa Real Madrid mai rike da kofin tana ta hudu da maki 31.
Barcelona za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na 18 a ranar 7 ga watan Janairun 2018, a kuma ranar ce Real Madrid mai kwantan wasa daya za ta ziyarci Celta Vigo.
Source: BBC Hausa
Title :
Barca Ta Baiwa Madrid Tazarar Maki 14
Description : Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 3-0 a wasan mako na 17 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu da suka kara a ranar Asa...
Rating :
5