Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba ya fargabar dawowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar jam'iyyar PDP, za ta kawo cikas a burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2019.
Sule Lamido ya fadi hakan ne a wata hira da suka yi da Haruna Tangaza na BBC, inda ya ce yana maraba da dawowar Atiku PDP don dama can jam'iyyar ce ta haife shi.
"Abun da aka yi wa Atiku Abubakar na daukaka da karamci a PDP ai ba a yi masa irinsu a APC ba, don haka mene ne laifi don ya dawo gida?" In ji Suke Lamido.
Da yake Sule Lamido ya jima da bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takara a inuwar jam'iyyar PDP, sai Haruna Shehu Tangaza ya tambaye shi shin ko dawowar Atikun ba ta dagula masa lissafi ba?
"Babban burinmu PDP ta tsayar da dan takara nagari wanda 'yan Najeriya ke so, don haka babu wani abun damuwa, a takaice ma so nake duk 'yan PDP da suka fice to su dawo, tun da dai Atiku ya dawo," in ji shi.
Ya kara da cewa: "So nake duk su Wamakko su Kwankwaso su AbdulFatah su Saraki su Abdullahi Adamu, kuma na tabbata duk za su dawo. Ya kamata a gane cewa su wadannan mutanen duk sun samu sunansu da kwarjininsu a PDP ne.
"Komawarsu APC cin mutuncinsu ne, wulakantasu ne kuma cin mutuncin tarihinsu ne".
Sule Lamido ya kuma mayar wa jam'iyyar APC martani a kan yadda take cewa duk 'yan PDP masu cin hanci da rashawa ne, inda ya ce duk barayi da kazaman jam'iyyarsa ta PDP ne suka kafa gwamnatin jam'iyyar APC.
"An shafe shekaru jam'iyyar APC na takara a kasar amma ba ta samu nasara ba sai da "wadannan barayi kazaman 'yan PDP suka koma suka yi wa APC ciki, sannan aka haifi gwamnatin APC ta yanzu."
"Duk masu cewa 'yan PDP barayi ne, to ai ga shi nan ai barayin ne suka je suka yi cikin wannan gwamnatin har aka samar da 'yar barauniya. Don haka don da ya zagi uwarsa mene ne laifi?" a cewar Sule Lamido.
Ya kara da cewa yana mamakin yadda don kawai a baya mutum yana jam'iyyar PDP sai ya koma APC sai a dinga ganin kamar ya zama wani waliyyi.
"Ga misali lokacin da Atiku yake APC duk an yi shiru, amma yanzu da ya dawo PDP sai aka aka fara zaginsa.
"A tsarin 'yan APC babu siyasa sai fushi da gilla da cin mutunci babu maganar sanin kasa."
Dawowar Atiku Abubakar jam'iyyar PDP dai a baya-bayan nan, ta sa masu sharhi na ganin za a kai ruwa rana tsakaninsa da Sule Lamido don a bayyane take cewa Atikun ya koma jam'iyyar ne domin neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019.
Source:BBC Hausa
Title :
Barayin PDP Ne Suka Kafa APC-Sule Lamido
Description : Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba ya fargabar dawowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ...
Rating :
5