Arsene Wenger ya ce ba shi da wata damuwa a kan rasa Alexis Sanchez a watan Janairu, duk da kwallo biyu da dan wasan na gaba ya ci wa kungiyar da ta doke Crystal Palace 3-2.
Kwantiragin dan wasan na Chile zai kare ne da Arsenal a karshen kakar da ake ciki, kuma ana danganta dan wasan mai shekara 29 da tafiya jagorar Premier Manchester City, wadda ta kasa sayensa a karshen kakar da ta gabata.
Wenger wanda ya kamo tarihin da Sir Alex Ferguson ya kafa a Premier na jagorantar wasa 810 a gasar, ya ce shi kam ba shi da wata damuwa, illa dai abu ne da ya shafi kwantiragin dan wasan.
A wasan nasu da Newcastle bayan Andros Townsend ya farke kwallon da Shkodran Mustafi ya ci wa Arsenal a kashin farko na wasan ne, Sanchez ya zura kwallo biyu a cikin minti hudu a ragar masu masaukin bakin.
Mustafi ya fara daga ragar 'yan Newcastle a minti na 25 da wasa, amma Townsend ya farke a minti na 49, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ke nan.
Daga nan ne kuma sai Sánchez din ya ci wa Arsenal ta biyu a minti na 62, sannan ya kara daga ragar bayan minti hudu.
Ana shirin tashi ne daga wasan sai kuma Tomkins ya ci wa Newcastle ta biyu a minti na 89.
Nasarar ta sa Gunners din sun ci gaba da zama a matsayi na shida da yawan maki 37 daidai da ta biyar Tottenham, kuma maki daya tsakaninta da ta hudu Liverpool.
Ita kuwa Newcastle tana matsayi na 16 a teburin na Premier bayan wasa 20.
Source: BBC Hausa
Title :
Bana Tsoron Ficewar Sanchez Daga Kulob Dinnan Duk Da Cin Kwallon Dayake-Wenger
Description : Arsene Wenger ya ce ba shi da wata damuwa a kan rasa Alexis Sanchez a watan Janairu, duk da kwallo biyu da dan wasan na gaba ya ci wa kungiy...
Rating :
5