Kotin Moscow ta yanke wa tsohon ministan tattalin arzikin Rasha Alexei Ulyukayev hukuncin daurin shekara takwas a gidan yari bisa laifin cin hanci.
Har ila yau an ci tarar shi fiye da fam miliyan daya. Shi ne minista na farko da aka taba yankewa hukunci tarihin Rasha na baya-bayan nan.
An kama Ulyukayev mai shekara 61 a shekarar 2016, inda aka tuhumeshi da kokarin yin almundahana na dala miliyan biyu daga kamfanin mai mallakin gwamnati.
boss ne ya tuhumeshi, na hannun daman shugaba Vladimir Putin.
Rosneft boss Igor Sechin ya bukaci ya gabatar shaida amma ya gaza hakan.
Allkali ne ya karanto hukunci inda yake cewa"Ulyukayev ya yi amfani da mukaminsa don ya bukaci cin hanci daga Rosneft chief Sechin, ta hanyar musayar bayar da amincewa, a kan sayar da kamfanin mai da gas na Bashneft mallakin gwamnati.
Mr Feoktistov ya ce, Mr Sechin ya shaida masa cewa "Amfani da yatsu biyu da ya yi ya nuna cewa kudin da ya bukaci ya karba sun kai dala miliyan biyu.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyanke Wa Tsohon Ministan Hukunci Daurin Shekara 8 A Gidan Yari
Description : Kotin Moscow ta yanke wa tsohon ministan tattalin arzikin Rasha Alexei Ulyukayev hukuncin daurin shekara takwas a gidan yari bisa laifin cin...
Rating :
5