Wata kotun soji a Najeriya ta yanke hukuncin kisa a kan wani jami'in sojin kasar bayan kama shi da laifin kisan wasu fararen hula a yankin arewa maso gabashi da ake yaki da Boko Haram.
Kotun sojin ta musamman a Maiduguri ta zartar da hukuncin ne kan koforal John Godwin da ta samu da laifin kisan fararen hula biyar da sojoji suka kubutar a garin Yamteke.
Jami'in wanda yana cikin rundunar Lafiya Dole da ke fada da Boko Haram, ya harbe mutanen ne a garin Maiduguri, a yayin da ake tsare da su domin amsa tambayoyi.
A cikin sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar ta ce kotun ta kuma daure wani jami'in soja rai da rai mai suna Innocent Ototo wanda kotun ta samu da laifin azabtarwa da kisan wani yaro dan shekaru 13 bayan jami'in ya zarge shi da sace wayarsa ta salula a Maiduguri.
Sannan kotun ta kuma zartar da hukuncin daurin shekaru 20 a kan wasu jami'an soja guda biyu kan laifin kisa da mallakar makamai ta hanyar da ba ta dace ba.
Rundunar sojin Najeriya ta ce laifukan da jami'an suka aikata sun saba dokokin kasa da na duniya.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na gida da na waje dai sun dade suna zargin sojojin Najeriya da kashewa da kuma cin zarafin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, zargin da rundunar sojin kasar ta sha musantawa.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyanke Ma Wani Sojan Nijeriya Hukuncin Kisa
Description : Wata kotun soji a Najeriya ta yanke hukuncin kisa a kan wani jami'in sojin kasar bayan kama shi da laifin kisan wasu fararen hula a yank...
Rating :
5