Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta umarci kociyan Manchester United Jose Mourinho da ya fayyace mata wasu kalamai da ya yi kafin wasansu na hamayya na ranar Lahadi wanda Manchester City ta doke su 2-1.
Hukumar ta bukaci hakan ne kan maganganun da ya yi a lokacin taron manema labarai na shirye-shiryen tunkarar wasan, a ranar Juma'a.
A lokacin Mourinho, wanda aka ba wa wa'adin zuwa karfe 6:00 na yamma agogon GMT, ranar Litinin ya bayar da bayani, ya ce 'yan wasan City suna da saurin faduwa, ta yadda ko da iska ce 'yar kadan ta taba su sai su je kasa.
Mourinho, mai shekara 54, ya kuma ce ba ya jin za a bar shi ya yi wasu kalamai na siyasa a filin wasa kamar Guardiola, wanda a kwanan nan aka gan shi ya sanya wata roba mai ruwan dorawa a hannunsa, ta alamar nuna rashin goyon baya kan tsare masu rajin neman 'yancin yankin Catalonia na Spaniya.
United ta yi rashin nasara a wasan da City da ci 2-1 a Old Trafford, ya zamanto abokan hamayyar sun ba ta tazarar maki 11 a teburin na Premier.
A yayin bureden murnar cin United din aka je fi Mourinho da ruwa da madara a kofar dakin sauya tufafi na 'yan City lokacin sa-in-sa tsakaninsa da golan bakin Ederson, dan Brazil, game da korafin da kociyan yake yi kan wuce makadi da rawa da yake ganin sun yi a lokacin murnar.
Kociyan dan Portugal daga baya ya bayyana wannan abu da 'yan City suka yi da cewa matsala ce ta bambancin dabi'a da kuma bambancin ilimi.
Source: BBC Hausa
Title :
Antuhumi Mourinho Akan Man City
Description : Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta umarci kociyan Manchester United Jose Mourinho da ya fayyace mata wasu kalamai da ya yi kafin wasansu na h...
Rating :
5