Gwamnatin Amurka ta kara sanyawa wasu manyan jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu su biyu takunkumi, saboda rawar da suka taka a shirin samar da makami mai linzami a kasar.
A makon da ya gabata ne dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da sunayen jami'an, a lokacin da ta Majalisar ke zama na musamman.
Rahotanni sun ce Kim Jong-Sik ya taka rawa wajen samar da makami mai linzami wanda ke aiki da sinadarai masu karfi kamar dutse ba ta hanyar amfani da sinadari masu ruwa ba.
Shi kuwa Ri Pyong-chol an same shi da bai wa kasar kwarin gwiwar samar da wasu makamai masu linzami manya da kanana ne fita a jikinsu ya yin da aka harba shi.
A nata bangaren Rasha ta gargadi Amurka da ta guji matsawa Koriya ta Arewa lamba, dan kaucewa wani rikicin, ya yin da ta maimakon takalar fada kamata ya yi a sanya lokacin tattaunawa dan magance rikici tsakanin kasashen biyu.
Tun da fari, Shugaban Amurka Donald Trump ya jinjina wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri.
A wani sako da ya rubuta a shafinsa na twitter, Mr Trump ya ce hakan ya jaddada cewa duniya na bukatar zaman lafiya ne ba kashe-kashe ba.
A cewar Amurka, Koriya ta Arewa ta shigar da gangar tattacen man fetur miliyan 4 da rabi a shekarar 2016.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansawa Jami'an Koriya Ta Arewa Takunkumi
Description : Gwamnatin Amurka ta kara sanyawa wasu manyan jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu su biyu takunkumi, saboda rawar da suka taka a shirin sama...
Rating :
5