Rundunar sojin Najeriya ta sauke kwamandan da ke jagorantar yaki da kungiyar Boko Haram a kasar daga kan mukaminsa.
Hakan ya biyo bayan yawan hare-haren da 'yan kungiyar ke kai wa ne a baya-bayan nan, wadanda suka hada da wani hari da aka kai masallaci a garin Mubi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 50.
Ba a dai bayar da wani dalili a hukumance na sauke Manjo Janar Attahiru Ibrahim ba.
Babban hafsan rundunar sojin kasa Tukur Buratai, ya ba shi wa'adi a watan Yuli don ya kawo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a raye ko a mace cikin kwana 40.
A kalla mutum 20,000 aka kashe, yayin da kungiyar ta sace wasu dubbai, tun lokacin da kungiyar ta fara ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama mulki ne a watan Mayun 2015, inda ya yi alkawarin murkushe mayakan.
Bayan wata bakwai da hawansa ne, ya ayyana cewa an yi nasara a yaki da kungiyar, bayan da sojoji suka kwato mafi yawan yankunan da ke karkashin ikon mayakan.
Sai dai kuma Boko Haram ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a arewa maso gabshin kasar.
A watan Yuli ma, fiye da mutum 40 ne suka mutu a yayin wani aiki da sojoji suka yi don tserar da mutanen da mayakan Boko Haram suka yi wa kwanton-bauna a wani ayarin motoci.
Wadanda suka mutun sun hada da sojoji da wata tawagar masu hakao mai.
An nada Manjo Janar Attahiru Ibrahim ne don ya jagoranci yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya a watan Mayun wannan shekarar.
Ya maye gurbin Janar Nicholas Rogers ne, wanda ya jagoranci wata rundunar hadin gwiwa ta musamman ta sojoji da 'yan sanda, don dakile rikicin kabilanci a yankin tsakiyar Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansauke Kwamadan Rundunar Yaki Da Boko Haram
Description : Rundunar sojin Najeriya ta sauke kwamandan da ke jagorantar yaki da kungiyar Boko Haram a kasar daga kan mukaminsa. Hakan ya biyo bayan yaw...
Rating :
5