Majalisar Duniya ta ce, an samu karuwa a yawan matasa da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar HIV a kasashen da ke yammaci da kuma tsakiyar Afirka.
A cikin wani sabon rahoto da UNICEF da kuma UNAIDS suka fitar sun ce, a cikin yara biyar da ke dauke da kwayar cutar HIV, hudu daga cikinsu basa samun maganin da ke rage yawan radadin cutar.
Majalisar Dinkin Duniyar, ta ce kasashen da ke yammaci da kuma Tsakiyar Afirka sune a baya a yakin da ake yi da cutar HIV/AIDS wajan samar wa yara da kuma manya magungunan da ke rage radadin cutar.
Shugaban asusun kula da yara ya ce yanayin da ake ciki abin takaici ne.
Kashi 25 cikin dari na yara da ke yankin na dauke da cutar HIV.
Rahoton na UNICEF da kuma UNAIDS ya ce, kasashe da dama a Afrika basu da isasun kayan aiki da ake bukata wajan yi wa jarirai gwaji.
Haka kuma matasa da ke yankin na cikin mawuyacin hali.
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon kamuwa da cutar HIV ya karu da kashi 35 daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2016 a tsakanin matasa masu shekara 15-19.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya yin da yawan matasa zai karu a kasashe irinsu Jamhuriyar Dimukradiyar Congo da kuma Nigeria za a ci gaba da samun karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da kuma mutuwa daga cutar HIV.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansamu Karin Matasa Masu Cutar HIV A Yammacin Afrika
Description : Majalisar Duniya ta ce, an samu karuwa a yawan matasa da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar HIV a kasashen da ke yammaci da kuma tsakiyar A...
Rating :
5