Masu garkuwa da mutane a teku sun sace ma'aikatan wani jirgin ruwan 'yan kasuwa su 10 a kusa da gabar tekun yankin inji rahotanni daga yankin Neja Delta.
Hukumar kasa da kasa mai kula da zurga-zurgar jiragen ruwan kasuwanci ta ce lamarin ya auku ne kusa da Brass da ke cikin jihar Bayelsa.
Kafofin watsa labarai a yankin sun ruwaito cewa mahara shida ne suka fara kai wa jirgin hari kafin daga baya suka kutsa cikinsa, inda suka sace ma'aikatan jirgin.
Babu rahoton cewa an raunata wani a lokacin harin amma sauran ma'aikatan da ke kan jirgin ruwan sun sami damar isa wata tashar jirgin ruwa inda suka sami mafaka.
Ba a bayyana asalin kasashen mutanen da aka sacen ba.
Yankin gabar tekun Neja Delta mai arzikin fetur ya yi kaurin suna wajen satar mutane da garkuwa da su domin neman kudin fansa a yammacin Afirka.
Rundunar sojin ruwan Najeriya ba su tabbatar da aukuwar lamarin ba, amma masana harkokin sufurin ruwa a yankin sun ce an sami karuwar hare-hare a makwannin da suka gabata.
Kawo yanzu an sami rahoton hare-hare akalla guda 15.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cibiyar Sea Guardian na cewa an sace kimanin ma'aikatan jiragen ruwa 56 a bana kawai.
A watan Oktoba ma an sace wasu mutum shida daga wani jirgin ruwa mai jigilar kaya mallakin Jamus kusa da yankin hada-hadar man fetur na Fatakwal.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansace Mutum 10 Daga Jirgin Ruwansu A Niger Delta
Description : Masu garkuwa da mutane a teku sun sace ma'aikatan wani jirgin ruwan 'yan kasuwa su 10 a kusa da gabar tekun yankin inji rahotanni da...
Rating :
5