Hukumomi a China sun rufe wata makaranta da ke koya wa mata biyayya ga maza su kuma zama masu mika wuya da barin mazansu yin iko da su.
Hukumar ilimi ta ce makarantar, wacce ke koyar da dabi'un al'ada, tana yin karan-tsaye ga akidun ci gaba zamani.
Wani bidiyo a kafar intanet ya nuna malaman makarantar na kushe batun daidaiton jinsi, suna kuma ce wa matan ka da su taba dukan miji ko da kuwa shi ne ya fara dukansu.
Ana samun karuwar irin wadannan makarantu a China a shekarun baya-bayan nan.
Bidiyon, wanda ya yadu kamar wuta-daji a intanet, ya nuna malamai a makarantar koyar da al'adu ta Fushon, suna cewa mata ka da su yarda su nemi wani aiki ko kokarin zama wani abu a rayuwa, 'kawai su kasance a karkashin maza.'
Suna kira ga mata cewa su yi wa iyayensu maza da mazajensu da 'yan'yansu maza ladabi da biyayya a ko wanne irin yanayi.
Wasu shawarwarin da makarantar ke bayar wa sun hada da cewa ka da su taba yin sa'insa da maza ko da an muzanta su ne, kuma ka da su taba neman saki.
An kuma ga malaman suna gargadin mata cewa idan mace ta sadu da fiye da maza uku, to maniyyinta ya zama guba, kuma zai iya kashe ta.
"Duk abun da mijinki ya nema, to ka da ki ce a'a," in ji daya daga cikin malaman.
Bidiyon ya nuna yadda mata ke aikin gida kamar goge dandaryar kasa da goge bandaki da hannunsu.
Jaridar Global Times ta ruwaito cewa, ma'aikatan makarantar da dama sun yi zanga-zangar rufe ta da aka yi, inda suka shaida wa jaridar cewa, an yi wa bidiyon kwaskwarima ne don bata aikinsu na gyaran al'ada da suke yi.
A yanzu dai hukumomi sun bayar da umarnin yin bincike don gano ko akwai wasu makarantun irin wannan.
Sanarwar da hukumomi suka fitar ta ce: "Dole mu dakatar da irin wadannan makarantu don sun kaucewa akidun ci gaba na zamani."
An bude wannan makaranta ne a shekarar 2011.
Source: BBC Hausa
Title :
Anrufe Makarantar Koya Wa Mata Biyayya A China
Description : Hukumomi a China sun rufe wata makaranta da ke koya wa mata biyayya ga maza su kuma zama masu mika wuya da barin mazansu yin iko da su. Huk...
Rating :
5