Zuciyar wasu tsoffin ma'aurata ta sosu kwarai da gaske a Canada, bayan da suka samu labarin cewa za a raba su a karon farko a cikin shekara 70, kuma mako guda kafin bikin Kirsimeti.
An dai shaida wa Herbert Goodine, mai kimanin shekara 91, cewa zai bar gidan kula da tsofaffi da suka shafe lokaci mai tsawo tare da matarsa Audrey Goodine,mai kimanin shekara 89, a ciki inda za a kai shi gidan kula da marassa lafiya.
Masu kula da gidan tsoffin sun shaida wa masoyan junan cewa a cikin makonnan za a mayar da Mr Goodine.
Wannan labari dai ya harzuka mutanen a sassan kasar nan.
'Yar ma'auratan Dianne Phillips, ta rubuta a shafinta na Facebook cewa " Da na ke magana da iyayena ta waya, na ji mahaifiyata na ta kuka, ban ji alamun mahaifina a kusa da ita ba".
'Yar ta ci gaba da cewa, mahaifiyata ta shaida mini cewa su fa bikin Kirsimeti a wajensu ya kare, kuma wannan shi ne bikin da bai zo musu cikin dadi ba, me ya sa ba za a bar mini maigidana sai bayan wannan biki ba?
Mrs Phillips, ta ce an kirata daga gidan kula da tsoffin inda ka ce mata mahaifinta baya jin dadi don haka za a kai shi gidan kula da marassa lafiya domin ya samu kulawa sosai.
Source: BBC Hausa
Title :
Anraba Ma'aurata Bayan Shekaru 70 Tare
Description : Zuciyar wasu tsoffin ma'aurata ta sosu kwarai da gaske a Canada, bayan da suka samu labarin cewa za a raba su a karon farko a cikin shek...
Rating :
5