Rundunar 'yan sandan jihar Kogi da ke Najeriya ta ce ta kori jami'anta uku da take zargi da laifin fatauncin wiwi.
Kakakin rundunar ASP William Aya ya tabbatar wa BBC cewa jami'an hukumar hana sha da fataucin kwayoyi, NDLEA ne suka kama 'yan sandan a watan Nuwamba lokacin da suke yin rakiya ga wata mota dauke da buhu 30 na wiwi a Lokoja, babban birnin jihar.
Ya kara da cewa hukumar NDLEA ce za ta gurfanar da su a gaban kotu.
A cewar ASP Aya, rundunar 'yan sanda ba za ta lamunci duk wani jami'inta da zai bata mata suna ba.
Ana zargin 'yan sandan kasar da yin kaurin suna wajen aikata laifukan da suka kamata su hana aikatawa, ko da yake sun sha musanta zargin.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankori Yan Sanda Masu Fataucin Wiwi
Description : Rundunar 'yan sandan jihar Kogi da ke Najeriya ta ce ta kori jami'anta uku da take zargi da laifin fatauncin wiwi. Kakakin rundunar...
Rating :
5