An samu gawar wasu attajirai miji da mata 'yan kasar Canada a cikin gidansu da ke birnin Toronto, a cikin wani yanayi da 'yan sanda suka bayyana a matsayin "ba mutuwar Allah da Annabi ba ce."
Mista Sherman shi ne wanda ya samar da kamfanin hada magunguna na Apotex kuma shi ne shugaban kamfanin.
Yana daya daga cikin manyan masu kudin Canada kuma wanda ya shahara a taimaka wa mutane.
A wani bayani da aka fitar a yammacin Juma'a 'yan sanda sun ce ba a samu wata alama da take nuna da karfi aka shiga cikin gidan ba.
Kafar sadarwa ta kasar sun bayar da rahoton cewa masu bincike ba su gudanar da bincike a kan neman wanda ake zargi a lokacin ba.
Detective Brandon Price ya shaida wa kafar watsa labarai ta kasar (CBC ) cewa, har yanzu masu bincike na kokarin gano ko akwai wanda yake da hannu a cikin lamarin.
'Yan sanda sun bayar da bayani kadan kuma ba su tabbatar da shaidun matattun ba.
Kodayake, abokai da jami'ai sun ambato sunan wasu da suka nuna razana da tashin hankali da suka ji labarin.
Ministan lafiyar kasar Eric Hoskins ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, "Ba ni da wani abu da zan iya fada a wannna lokacin".
Ya kuma kara da cewa, "An samu abokaina Barry da Honey Sherman a mace. Mutane masu kirki, masu taimakawa jama'a, manyan jagorori a fagen magani".
Mai magana da yawun 'yan sanda ya ce, an kira masu taimakon gaggawa gidan ranar Juma'a.
Constable David Hopkinson ya ce,"yanayin mutuwarsu ya nuna cewa akwai lauje cikin nadi kuma muna bin al'amarin".
Toronto Globe and Mail ya bayar da rahoton cewa, kwanan nan ne ma'auratan suka saka katafaren gidansu a kasawa, sai kuma dillalen gidaje ya tarar da gawarsu lokacin da ya zo ganin gidan,
Mamatan sun bar 'ya'ya hudu.
Mista Sherman ya kama kamfaninsa ne a shekarar 1974, kuma yanzu shi ne na bakwai wajen hada magani a duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe Wani Attajiri Da Matarsa A Canada
Description : An samu gawar wasu attajirai miji da mata 'yan kasar Canada a cikin gidansu da ke birnin Toronto, a cikin wani yanayi da 'yan sanda ...
Rating :
5