Kungiyoyin kare hakkin bil'dama da 'yan jarida da kuma jami'an MDD sun riga sun tattara bayyanai daga 'yan gudun hijira da suke samun mafaka a kasar Bangladesh akan cin zarafi mai tayar da hankali, da suke zargin jami'an tsaron Myanmar sun yi a jihar Rakhine.
Sai dai wannan shi ne karon farko da ake samun binciken da ya samar da cikakken bayyani kan yawan musulmi 'yan Rohingya da aka kashe a tashin hankalin da ya barke sakamakon jerin hare haren da mayakan sa kai yan Rohinja suka kai a watan Augustan daya gabata
Lamarin ya sa sojoji suka kai mummunan farmakin da MDD ta bayyana a matsayin kawarda wata kabila daga doron kasa.
Kungiyar agaji ta likitoci ta Medicine san frontiers ta gudanar da bincike guda shida a watan daya gabata a sansanonin 'yan gudun hijira , inda ta yi magana da mutane dubu biyu da dari biyar .
Ta gano cewa mace macen da aka yi musaman tsakanin yara a mafi yawan lokuta ya zarta yadda ake tunani kuma kashi sabain cikin dari na mace macen sun faru ne a tashin hankalin, da ya faru.
MSF ta kuma ce akasarin su sun rasa rayukansu ne daga raunukan da suka ji daga harbin bindiga, adadin da ya zarta kiyasin da aka fitar tun farko.
Sai dai wannan rahoton zai karfafa kiraye kirayen da wasu suke yi akan cewa ya kamata a binciki hukumomin Myanmar game da zargin cin zarfin bil'adama.
Rundunar sojin Myanmar din dai ta riga ta gudunar da bincike kan zargin da ake yi ma sojojin kasar kuma ta ce sojojinta basu aikata laifi ba.
Har yanzu masu bincike daga MDD da kuma kungiyoyi agaji basu sami damar zuwa jihar Rakhine ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe Musulmi 6,700 A Myanmar
Description : Kungiyoyin kare hakkin bil'dama da 'yan jarida da kuma jami'an MDD sun riga sun tattara bayyanai daga 'yan gudun hijira da s...
Rating :
5