Filin Wembley zai karbi bakuncin wasa bakwai a lokacin gasar cin kofin kasashen Turai ta 2020, bayan da birnin Brussels ya rasa damar karbar bakuncin wasannin gasar.
Babban birnin na kasar Belgium ya rasa damar ne saboda sabon filin da aka tsara za a gina a can har yanzu ba a yi shi ba, kuma hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa ba ta samu wani tabaci na kammala shi ba kafin lokacin.
Daman an tsara za a yi wasannin kusa da karshe da kuma na karshe a filin Wembley, to amma kuma a yanzu za a kara masa da wasanni uku na rukuni da kuma guda daya na zagayen kungiyoyi 16.
Cardiff da Stockholm ma sun kasance cikin masu neman karbar bakuncin karin wasannin gasar.
Babban filin wasan na Ingila wato Wembley na daya daga cikin filin wasanni 12 a fadin Turai da za su karbi bakuncin gasar ta cin kofin kasashen Turai, ta Euro 2020.
Da yake jawabi a hedikwatar hukumar kwallon kafa ta Turai, da ke birnin Nyon, shugaban na Uefa Aleksander Ceferin , ya ce shawarar da aka yanke ta samu amincewar dukkanin 'yan kwamitin zartarwa na hukumar.
Gasar ta cin kofin Turai ta 2020, wadda za a fara daga ranar 12 ga watan Yuni har zuwa 12 ga watan Yuli na shekarar, ita ce gasar Turai ta farko da za a yi bisa sabon tsarin da za a yi wasannin rukuni-rukuni a kasashen nahiyar daban-daban.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankarbe Wasan Kofin Turai Daga Brussels Zuwa Wembley
Description : Filin Wembley zai karbi bakuncin wasa bakwai a lokacin gasar cin kofin kasashen Turai ta 2020, bayan da birnin Brussels ya rasa damar karbar...
Rating :
5