'Yan sandan Ghana sun yi barzanar gurfanar da duk wanda ya yi amfani da tartsatsin wuta mai hatsari a lokacin bukukuwan Kiristimeti domin kare rayukan jama'a.
An haramta amfani da tartsatsin wutan ne bisa la'akari da wata dokar shekarar 1999, kuma an bai wa jami'an tsaro umarnin kama "duk wani mutum ko kuma mutane" da suka ki bin umarnin hana amfani da tartsatsin, in ji wata sanarwar da mataimakin kwamishinan 'yan sanda David Eklu ya fitar.
A wata hira da wakilin BBC, ya kara da cewa "mutane da dama suna tunanin cewa wannan dokar ta daina aiki, amma muna amfani da wannan damar domin tabbatar wa mutane cewa za mu kaddamar da dokar yadda ya kamata.
"Wannan ba zai dauke farin cikin bikin Kiristimeti ba domin tartsatsin wuta mai hatsari kawai aka haramta amfani da shi. Ya fi dacewa ka kare kanka da makwabtanka, a kan ka samu kanka a asibiti a lokacin Kiristimeti."
Source: BBC Hausa
Title :
Anhana Wasan Wuta A Ghana Lokacin Kirismeti
Description : 'Yan sandan Ghana sun yi barzanar gurfanar da duk wanda ya yi amfani da tartsatsin wuta mai hatsari a lokacin bukukuwan Kiristimeti domi...
Rating :
5