Yan sandan Saudiyya sun ce sun gano gawar wani alkalin da aka sace shekara daya da ta wuce.
An gano gawar Sheikh Mohammed al-Jirani ne bayan wani artabu a makon da ya wuce tare da wasu da ake zargin 'yan gwagwarmaya ne a wata gona a gabashin kasar.
Alkalin, dan shi'a ne tsiraru da ke birnin Awamiya a kasar Saudiyya da ke korafin cewa 'yan sunna masu rinjaye sun mayar da su saniyar ware.
Sheikh Jirani dai ya sha sukar zanga-zangar da 'yan shi'a ke yi, kuma ya zargi manyan malamai a cikin al'ummar shi'a din da kasancewa kut-da-kut da Iran.
A watan Disambar 2016 ne aka sace Sheikh Mohammed al-Jirani a gaban gidansa da ke birnin Awamiya.
A wancan lokacin hukumomi sun ce sun kama mutum uku da ake zargi da hannu a sace shin.
Kafofin yada labaran kasar sun ce dama an sha hakon alkalin a wasu hare-hare da aka sha kai wa kafin daga bisani a sace shi.
Source: BBC Hausa
Title :
Angano Gawar Wani Alkali Da Aka Sace A Saudiyya
Description : Yan sandan Saudiyya sun ce sun gano gawar wani alkalin da aka sace shekara daya da ta wuce. An gano gawar Sheikh Mohammed al-Jirani ne baya...
Rating :
5