Hukumomi a Najeriya na ci gaba da dawo da 'yan kasar gida wadanda suka je ci-rani a kasar Libya.
Kimanin mutum 144 ne na baya bayan nan aka mayar da su gida ranar Talata ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos.
Hukumomi sun ce yanzu haka akwai 'yan Najeriya kimanin 3,000 da aka tantance a sansanonin da ake tsare da 'yan ci-rani a Libya.
Wasu daga cikin 'yan Najeriyar da suka dawo gida a daren Talata sun shaida wa manema labarai irin bakar wahala da suka sha a Libya bayan da aka sayar da su a matsayin bayi.
A watan Nuwamba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ana sayar da 'yan kasar tamkar awaki a Libya.
Da yake jawabi ga 'yan Najeriya mazauna kasashen waje a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast, shugaba Buhari ya sha alwashin rage yawan 'yan kasar da ke yin ruguguwa wajen zuwa Turai.
Kungiyar tarayyar Afrika dai ta amince ta kwashe kimaniin 'yan cirani 15,000 daga Libya kafin karshen 2017.
Mataimakin shugaban hukumar tarayyar Afrika Kwesi Quartey ya wallafa a shafin sa na twitter cewa za'a kwashe 'yan ciranin ne tare da hadin guiwar kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM.
Source: BBC Hausa
Title :
Andawo Da 'Yan Nijeriya Daga Libya
Description : Hukumomi a Najeriya na ci gaba da dawo da 'yan kasar gida wadanda suka je ci-rani a kasar Libya. Kimanin mutum 144 ne na baya bayan nan...
Rating :
5