Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar kociyan Chelsea Antonio Conte fam 8,000, sama da naira miliyan hudu saboda laifin da ya aikata na ja da hukuncin alkalin wasa har aka kore shi zuwa cikin 'yan kallo a wasansu da Swansea a watan da ya wuce.
An kori Conte ne saboda nuna rashin yarda da hukuncin alkalin wasa Neil Swarbrick, wanda ya ki ba wa Chelsea wani bugun gefe (kwana), a wani lokaci na kashin farko na wasan.
Bayan wasan, wanda Chelsea ta yi nasara da ci 1-0, kociyan dan Italiya mai shekara 48 ya bayar da hakuri ga alkalin wasa Swarbrick.
Ya kuma kara da cewa ya yi kuskure. Yana shan wuya da 'yan wasansa. Abin takaici ne.
Chelsea tana matsayi na uku ne a teburin Premier, da tazarar maki 11 tsakaninta da jagora Manchester City.
Source: BBC Hausa
Title :
Anci Taran Conte Naira Miliyan Hudu
Description : Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar kociyan Chelsea Antonio Conte fam 8,000, sama da naira miliyan hudu saboda laifin da ya aikata na...
Rating :
5