Bayan da aka kammala wasannin mako na 19 a ranar Asabar a gasar cin kofin Premier ta bana, an ci kwallo 504.
Gasar wacce aka fara a ranar 11 ga watan Agustan 2017, wacce kungiyoyi 20 ke fafatawa sun buga wasanni 190 kawo yanzu.
'Yan wasa biyu ne ke kan gaba a yawan cin kwallo a raga, inda Harry Kane na Tottenham da Mohamed Salah na Liverpool kowannensu ya ci kwallo 15.
Wasan da aka fi cin kwallaye a gida shi ne wanda Manchester City 5-0 Liverpool, Manchester City 5-0 Crystal Palace, Manchester City 7-2 Stoke City da na Arsenal 5-0 Huddersfield Town.
Manchester City wacce ke mataki na daya a kan teburi ta ci wasa 17 a jere, ta kuma yi 19 ba a doke ta ba.
Ita kuwa West Bromwich Albion wacce take ta 19 a kasan teburi ta yi wasa 17 ba tare da ta yi nasara ba a kakar ta bana.
Za a shiga wasannin mako na 20 a ranar Talata 26 ga watan Disamba:
Chelsea da Brighton & Hove AlbionManchester United da BurnleyWest Bromwich Albion da EvertonWatfordda Leicester CityHuddersfield Town da Stoke CityBournemouth da West Ham UnitedLiverpool da Swansea CityTottenham da Southampton.
Source: BBC Hausa
Title :
Anci Kwallo 504 A Gasar Premier Ingila
Description : Bayan da aka kammala wasannin mako na 19 a ranar Asabar a gasar cin kofin Premier ta bana, an ci kwallo 504. Gasar wacce aka fara a ranar 1...
Rating :
5