Wani sabon bincike da aka gudanar ya gano cewa ana zubar da ciki fiye da miliyan 15 a India a kowacce shekara.
Wannan kididdiga dai ta dara wadda aka bayar a hukumance a kasar.
Wata cibiyar bincike mai suna Guttmacher Institute's research da ke New York, ta gano cewa mafi yawan matan Indian da suke zubar da cikin, suna amfani ne da kwayoyi ba bu ka'ida a gida ba tare da tuntubar yadda za a yi amfani da su ba.
Gwamnatin kasar ta India, ta ce ana zubar da ciki kasa da dubu 700 ne a kowacce shekara a kasar ne.
Gwamnatin ta samo adadin ne bayan ta hada bayanai daga asibitocin jihohi da kuma dakunan sha ka tafi.
Masu binciken sun ce matan kan sha wuya a yayin zubar da cikin.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Zubar Da Ciki Miliyan 15 Kowani Shekara A Indiya
Description : Wani sabon bincike da aka gudanar ya gano cewa ana zubar da ciki fiye da miliyan 15 a India a kowacce shekara. Wannan kididdiga dai ta dara...
Rating :
5