Ce-ce-ku-ce ya barke a shafukan sada zumunta da muhawarar Najeriya, kan nadin da gwamnan jihar Imo da ke kudancin kasar ya yi wa kanwarsa, na kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata.
A ranar Litinin ne Gwamna Rochas Okorocha ya nada sabbin kwamishinoni 28, da shugabannin kwamitin mika mulki 27 da kuma shugabannin kananan hukumomi 27 a jihar.
Mutane na ta tafka muhawara ne kan nadin da Mista Okorocha ya yi wa kanwar tasa, inda da dama ke ganin babu wani abun burgewa wajen kirkiro sabon matsayin na kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata, yayin da wasu kuma ke cewa bai kamata ya bai wa kanwar tasa Mrs. Ogechi Ololo nee Okorocha, mukamin kwamishiniya ba.
Misis Ololo dai mata ce ga wani injiniya Chuks, wanda dan majalisar wakilan tarayya ne, kuma ta rike mukamai da dama tun bayan zamowar dan uwanta gwamna a shekarar 2011, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Kafin a nada ta kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata dai, tana rike da mukamin mataimakiyar shugaban ma'aikatan gidan gwamnati da kuma mai ba da shawara ta musamman kan al'amuran cikin gida ga gwamnan.
Wannan batu na nadin da Mista Okorocha ya yi wa kanwar tasa a matsayin kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata, kusan shi ne ya mamaye kafofin sada zumunta a Najeriya a ranar Talata, musamman ma shafin Twitter.
Sai dai wasu sun kwatanta nadin da Mista Rochas ya yi wa kanwar tasa da cewa ko a kasashe irin su Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ma, an nada ministar jin dadi da walwala.
Amma da dama sun soki hakan da cewa UAE kasa ce da ta riga ta ci gaba kuma al'ummarta ba sa cikin kunci kamar a Najeriya.
Wannan ne dai karo na farko da aka taba bayar da irin wannan mukami na ma'aikatar jin dadi da walwalar ma'aurata, wanda jihar Imon ta yi.
A watan Octoba ma Mista Okorocha ya yi ta shan suka sakamakon gina mutum-mutumin shugaba kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma na tagulla tare da sanya wa wani titi sunansa, a matsayin karrama shi.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Sukan Rochas Kan Nada Kanwarsa Kwamishinan Walwalar Ma'aurata
Description : Ce-ce-ku-ce ya barke a shafukan sada zumunta da muhawarar Najeriya, kan nadin da gwamnan jihar Imo da ke kudancin kasar ya yi wa kanwarsa, n...
Rating :
5