Zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran sun cigaba a rana ta uku, inda rahotanni ke nuna cewa masu zanga-zangar sun fito a wasu biranen masu yawa.
Hukumomin kasar dai suna ta wa 'yan kasar kashedi game da fitowa ko shiga wannan jerin zanga-zangar.
A jami'ar birnin Tehran, masu zanga-zanga sun yi kira ga babban jagoran addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya sauka daga mukaminsa.
An kuma sami rahoton cewa wadanda suka fito sun yi arangama da 'yan sanda.
Amma masu zanga-zangar sun yi kunnen uwar shegu da kiran na ministan harkokin cikin gida dake cewa 'yan kasar su "guji tarurrukan da hukuma bata amince da su ba."
A halin yanzu dubban magoya bayan gwamnati sun fito titunan kasar suna tasu zanga-zangar ta nuna goyon baya ga hukumomin kasar.
Gwamnati ce take shirya wadannan zanga-zangar domin dakile kokarin masu adawa da gwamnatin, domin tunawa da mukushe masu zanga-zanga da suka fito shekara takwas da ta gabata a 2009.
Wannan zanga-zangar ta fara ne a arewa maso gabashin kasar ranar Alhamis domin tsadar rayuwa, kuma kawo Jumma'a ya bazu zuwa wasu manyan biranen kasar.
Yadda abin ya samo asali
Mutane da dama ne aka ruwaito sun shiga zanga-zangar a Rasht a arewaci da Kermanshar a yammaci da kuma yankunan Shiraz da Isfahan da Hamadan na kasar.
Da farko an fara zanga-zangar ne domin adawa da tsadar rayuwa, yanzu kuma ta rikide ta koma ta adawa da gwamnati.
Rahotanni sun ce an cafke wasu daga cikin masu zanga-zangar a Tehran babban birnin kasar.
Kamfanin dillacin labaran Iran ya ruwaito mataimakin gwamnan Tehran na cewa gungun mutane 50 ne suka hada gangamin, a wani babban dandalin tsakiyar birnin.
Tun da farko mataimakin gwamnan ya ce 'yan sanda za su tarwatsa gungun masu zanga-zangar.
Masu aiko da rahotanni sun ce zanga-zangar ta adawa da gwamnati ita ce mafi girma tun wacce aka taba gudanarwa a 2009 bayan babban zaben kasar mai cike da kalubale.
An ji masu zanga-zangar na cewa "Mutane na bara".
A birnin Mashhad da ke arewa maso gabashi ne aka gudanar da babbar zanga-zanga, inda aka cafke mutane 52.
An kira zanga-zangar ne ta kafofin sadarwa na intanet, duk da gwamnati ta yi kashedin shirya duk wani gangamin da ya sabawa doka.
Wasu hotunan bidiyo da aka yada a shafukan sadarwa na intanet sun nuna yadda masu zanga-zangar ke arangama da masu zanga-zanga.
Masu zanga-zangar na adawa ne da gazawar gwamnatin shugaba Hassan Rouhani kan magance matsalar hauhawan farashin kayayyakin masarufi.
Zanga-zangar ta rikide ta koma ta adawa da gwamnati tare da yin kiran a saki fursunonin siyasa da kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yi wa jama'a.
Masharhanta a gabas ta tsakiya sun ce zanga-zangar ta zo wa gwamnatin Iran ba-zata, wacce ba a saba gani ba.
Wani sakamakon binciken BBC game da Iran ya nuna cewa kashi kusan 30 na 'yan kasar na shiga hali na talauci a shekaru 10 da suka gabata.
Wasu na ganin kudaden ya kamata a ce an kashe domin inganta rayuwarsu, amma an koma ana hidimar yaki da kudaden a Syria da Yemen da Iraqi.
Sannan ana kashe makudan biliyoyi domin watsa farfagandar shi'a a sassan duniya
Shugaba Hassan Rouhani ya yi alkawalin cewa yarjejeniyar nukiliya da ya sanya wa hannu tsakanin Iran da manyan kasashen duniya za ta taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar idan har an cire ma ta takunkumai.
Tattalin arzikin kasar dai yanzu ya fara bunkasa kamar yadda aka samu sassauci a hauhawan farashin kayayyaki amma har yanzu kasar na fama da karancin masu saka jari yayin da alkalumman rashin aikin ya kai kashi 12.4.
Source: BBC Hausa
Title :
An Shiga Kwana Na Uku Ana Zanga Zanga A Iran
Description : Zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran sun cigaba a rana ta uku, inda rahotanni ke nuna cewa masu zanga-zangar sun fito a wasu biranen masu ya...
Rating :
5