Takardar biyan kudin amfani da wutar lantarkin da ta kai $284bn da aka aike wa wata mata a jihar Pennsylvania ta ba ta matukar mamaki... har sai da ta gano kuskure aka yi sannan hankalinta ya kwanta.
Mary Horomanski ta ce takardar ta nuna cewa dole ta biya kudin kafin karshen watan Nuwambar shekarar 2018.
"Lamarin ya firgita ni sosai," in ji matar, a hirar da ta yi da jaridar Erie Times-News. "Mun kunna wutar lantarki ta bikin Kirsimeti kuma mun yi zaton mun kunna ne bisa kuskure."
Daga bisani kamfanin samar da hasken wutar lantarkin ya ce $284.46. ne hakikanin kudin da ya kamata matar ta biya.
Kakakin kamfanin ya ce bai san yadda aka tafka wancan kuskuren ba, yana mai cewa ba don an gano kuskuren ba da sai Ms Horomanski ta $284,460,000,000 inda za ta soma biyan $28,176 a matsayin kashin farko a watan nan na Disamba.
" Ban taba ganin an aike wa wani ko wata takardar kudin wuta da ta kai ta dala biliyan daya ba," in ji Mark Durbin a tattaunawarsa da Erie Times-News.
"Mun ji dadin yadda matar ta tuntube mu bayan ta ga takardar da aka aike mata bisa kuskure."
Source: BBC Hausa
Title :
An Nemi Wata Mata Ta Biya $284 Kudin Wutan Lantarki
Description : Takardar biyan kudin amfani da wutar lantarkin da ta kai $284bn da aka aike wa wata mata a jihar Pennsylvania ta ba ta matukar mamaki... har...
Rating :
5