Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da babbar murya ga wani kuduri da ya yi kira ga Amurka ta janye amincewar da ta yi wa Qudus ya zamo babban birnin Isra'ila.
Kudurin ya ce duk wata shawara da ke nuna cewa Qudus ne babban birnin Isra'ila ba za ta karbu ba kuma dole a hana aiwatar da ita.
Kasashe 128 ne suka amince da wannan kuduri da ba dole ne Amurkar ta yi aiki da shi ba, yayin da kasashe 35 suka kauracewa zaman majalisar, kana kasashe tara suka yi watsi da shi.
An dauki matakin ne bayan Donald Trump ya yi barazanar daina bayar da tallafin kudi ga duk kasar da ta amince da kudurin.
Kafin a amince da kudirin, ministan harkokin wajen Paladinu ya kori mambobin majalisar su yi fatali da abin da ya kira "bata suna da razanarwa".
Sai dai firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za su yi watsi da matakin ba tare da shakka ba sannan ya bayyana majalisar dinkin duniya a matsayin "gidan makaryata".
Source: BBC Hausa
Title :
Amurka Tasha Kaye Agun MDD Kan Birnin Kudus
Description : Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da babbar murya ga wani kuduri da ya yi kira ga Amurka ta janye amincewar da ta yi wa Qudus ...
Rating :
5